Ƴan Sanda Sun Hana Hakan Sallah Saboda Rikicin Masarautar Kano
Ƴan Sanda Sun Hana Hakan Sallah Saboda Rikicin Masarautar A Kano
Biyo bayan rikicin masarautar Kano da ya barke tsakanin sarki Muhammadu Sanusi ll da hambararren sarki Aminu Ado Bayero, rundunar ƴan sandan jihar Kano ta hana duk wani hawan daba na babbar Sallah a ɗaukacin jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a yau Alhamis, rundunar ta ce haramcin na daga cikin alkawurran samar da zaman lafiya da rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi tare da duk masu ruwa da tsaki a harkar tsaro.
“A ci gaba da haka, an sanya dokar hana yin bawan Sallah a fadin jihar domin gudanar da bukukuwan Sallah mai zuwa,” in ji shi.
Matakin da aka dauka, a cewarsa, “sakamakon jerin rahotannin tsaro da aka samu da kuma tuntubar juna da aka yi da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro domin tabbatar da tsaron lafiyar al’umma.”
Sai dai ya shawarci mazauna garin da su gudanar da Sallar Idi a wurare daban-daban da aka kebe don Sallar Idi, wanda aka saba yi a baya.
Sannan ya hori al’umma da su tuntubi rundunar idan su ka yi zargin wani yunƙurin tada hankali.