Kannywood

Ƙarƙuzu Yayi Godiya Ga Ahmed Musa Bayan Gina Mishi Gida

TSOHON ɗan wasan kwaikwayo, Malam Abdullahi Shu’aibu (Ƙarƙuzu ko Abdu Kano), ya yi wa shugaban ƙungiyar ƙwallo ƙafa ta Super Eagles, Ahmed Musa, godiya game da gida da ya saya masa a Jos, Jihar Filato.

Ahmed ya yi wa dattijon alƙawarin zai saya masa gida bayan mujallar Fim ta buga labarin halin ƙunci da ya ke ciki a gidan haya.

Matashin ɗan ƙwallon ya cika wannan alƙawari da ya ɗauka, ya saya wa Ƙarƙuzu gidan N5,500,0000. Da ma kuma tun farko ya ba shi kyautar N500,000 domin ya sayi abinci da magani.

A wata hira da ya yi da kafar yaɗa labarai ta ‘Zinariya TV’, wadda da ma ita ce ta fara yaɗa labarin cewa dattijon ya na neman taimako, dattijon ya yi wa Ahmed Musa kirari har da sa masa suna daren ‘Lailatul Ƙadiri’.

Ƙarƙuzu ya ce, “Assalamu alaikum wa rahamatullahi ta’ala wa barakatuhu. Jama’q, su na na Ƙarƙuzu na Bodara. Na zo ne filin da zan yi wa Ahmed, Ahmed ɗan ƙwallon duniya, ka ga ta kowa, taka tai wuyar gani ɗan Baba.”

“To Ahmed, ina da suna guda biyu, na farko dai Ahmed sunan ka, to ni kuma yanzu ga nawa, sunan ka daren ‘Lailatu Ƙadiri’. Kuma Ahmed, abin da ka yi min ya wuce in ce na gode, sai dai duk lokacin da aka yi sallah in yi maka addu’a.

“Ahmed kai ne gulungulan ta doki ba ka da ɓargo; hadari malfar duniya; sama ta yi wa yaro nisa.

“Ba zan taɓa mantawa da kai ba daga nan duniya har mu tafi lahira domin abin da ka yi min ba wanda ya yi min shi a wannan duniyar,’ sai kai.

“Ku ma jama’a da ku ka taimaka da wanda ya ke da niyyar taimaka min, da wanda ya ji daɗi, da wanda bai ji daɗi ba, Ubangiji Allah na roƙe ka, Allah ya saka mana da alkhairi. Kuma Allah ya saka wa wannan bawan Allah da alkhairi, har ƙarshen rayuwa tasa, ya na nan ya na taimakawa da ya gama, ya shiga lahira sai aljanna in-sha Allahu.

“Kuma na gode delegates ɗin ka da ka turo, sun yi rawar gani. Kuma ba zan fasa yi wa Rocky, mai suna na, Abdullahi Rocky, shi ma abin ya ke yi min, ya yi min, to shi ma Ubangiji maɗaukakin sarki Allah ya saka masa da alheri.”

Ya kuma ƙara da cewa, “To Zinariya TV, kun taka rawar gani. Duniya ta gan ni, ta tausaya min, Ahmed Musa ya saya min gida, wanda da a gidan haya na ke, amma yanzu in-sha Allahu, ina cikin gida na ko kuma zan shiga.

“To ku Zinariya TV’, ku ma ƙarshen magana ta da na ke muku, Allah ya ƙara rufa maku asiri, Allah ya ƙara muku soyayya da jama’a.”

 

Back to top button
error: Content is protected !!